Tawagar ‘yan wasan Najeriya ‘yan ƙasa da shekaru 20, Flying Eagles, za ta fara kare kambunta na Gasar WAFU B akan tawagar Black Satellites ta Ghana a ranar 27 ga watan Yuli a filin wasa na Lycée Scientifique de Yamoussoukro da ke ƙasar Côte d’Ivoire.
Idan za a iya tunawa dai a shekarar 2024 Flying Eagles ce ta doke Black Satellites 2-1 a wasan ƙarshe, inda ta lashe kofin.
A wasan ta na biyu, Flying Eagles wadda ta lashe gasar har sau 7, za ta kara ne da Junior Sparrow Hawks na Togo a filin na Lycée Scientifique a ranar 30 ga watan Yuli.
-
Abin da ya kamata ku sani game da Alkalin Wasan Karshe na Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026
-
FIFA za ta bai wa tawagar da ta lashe Gasar Kofin Duniya ta 2026 zobe na zakaru a karon farko
-
Abdul Maikaba ya za ma sabon kocin Bayelsa United
Flying Eagles za ta kammala wasannin rukuni na B da Young Stallions na Burkina Faso a ranar 2 ga watan Agusta, kuma a wannan filin.
Kocin tawagar, Abdu Maikaba, tare da ‘yan wasan sa za su bar Najeriya ranar Litinin bayan kammala horaswa da tantancewa na tsawon makonni a Abuja.
