An tabbatar da mutuwar sojojin Amurka biyu bayan wasu hare-hare da Iran ta kai a wani sansanin sojin Amurka da ke ƙasar Jordan.
Haka kuma, wani sojan guda ɗaya a halin yanzu ya ɓata , yayin da wasu hudu kuma suka ji rauni a hare-haren amma an riga an yi musu magani, kamar yadda Babban Kayan Tsaron Amurka na Tsakiya (CENTCOM) ya sanar a ranar Asabar.
“A ranar 17 ga watan Yuli, dakarun Amurka biyu a Jordan sun mutu a bakin aiki yayin da Babban Kayan Tsaron Amurka na Tsakiya (CENTCOM) da dakarun hadin gwiwa suke kare kai daga hare-haren makami mai linzami da na jirage marasa mataki (drone) na Iran. Bugu da kari, soja guda daya a halin yanzu ya bace,” in ji CENTCOM a shafinsa na X.
- Gasar Cin Kofin Dunuya ta 2026: Ingila ta lashetagulla a kan Faransa
- Fujimori ta zama mace ta farko da ta zama shugabar ƙasar Peru
- Katsewar Wutar Lantarki ta shafi jihohi shida a Arewacin Najeriya – TCN
Domin nuna girmamawa ga iyalansu, CENTCOM za ta ɓoye sauran bayanan, ciki har da sunayen jaruman da suka mutu, har sai bayan sa’o’i 24 da sanar da danginsu na kusa.”
Waɗannan mace-macen sun kawo jimillar jami’an Amurka da aka kashe tun farkon yakin zuwa 16, yayin da fiye da 400 kuma suka ji rauni. Jaridar PREMIUM TIMES ta rawaito cewa an samu asarar rayukan Amurkawa na farko ne a watan Maris bayan da wasu jiragen yaƙi na Amurka guda uku suka yi hatsari a Kuwait.
Sojojin Amurka uku ne suka mutu a hatsarin, yayin da wasu hudu suka ji rauni mai tsanani.
Bayan ‘yan sa’o’i kadan, makaman linzamin Iran suka kashe wani sojan Amurka guda ɗaya.
Sabbin asarar rayukan sun biyo bayan sabon farmakin da kasashen biyu (Amurka da Iran) ke kai wa juna.
Wannan jaridar ta taɓa rawaito kafafen yada labaran Amurka na cewa sojojin Amurka da dama sun ji rauni a hare-haren baya-bayan nan da Iran ta kai kan wani sansanin Amurka a Jordan.
Iran ta ci gaba da kai hari kan sansanonin Amurka da ke yankin Tekun Fasha a matsayin ɗaukar fanasarsu kan hare-haren da Amurka ke kai wa Iran.
CENTCOM ta sanar a baya cewa Amurka ta kai hare-hare a daren Juma’a, wanda hakan ya kasance dare na bakwai a jere da take kai hari.
Bayan haka, Babban Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, ya zargi Amurka da “saɓa yarjejeniyoyi akai-akai” da Tehran. Ya bayyana sa hannun Shugaba Donald Trump a matsayin “marar amfani kuma marar inganci.”