Ƙwallaye uku da Bukayo Saka ya ci sun taimaka wa Ingila ta samu mafi kyawun sakamako tun bayan 1966 a Gasar Cin Kofin Duniya, inda ta doke Faransa 6-4 a wasan neman matsayi na uku na Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.

Gabannin fara wasan, magoya bayan tawagar Ingila sun yi wa kocinsu Thomas Tuchel ihu akan yadda ake sukar dababararsa ta tsaron gida a wasan da suka sha kaye a hannun Argentina a wasan kusa da na karshe a ranar Laraba.

Bukayo Saka ne aka bashi kwallon da aka buga wasan da shi, inda ya zama dan Ingila na biyu da ya ci kwallaye uku a wasan matakin knockout na Gasar Cin Kofin Duniya bayan Geoff Hurst a wasan ƙarshe na 1966.
- A karon farko Messi da Yamal sun magantu kan hoton wanka
- Karambatta tsakanin Joshua da Itauma a Najeriya zai dauki hankalin duniya—Ezekiel Adamu
- Atlético Madrid ta ce Julián Álvarez ba na sayarwa ba ne
A yayin wasan, Kylian Mbappe ya ci ƙwallo biyu kuma a halin yanzu shine wanda ya fi kowa zira ƙwallaye a tarihin Gasar Cin Kofin Duniya da ƙwallaye 22 yayinda Lionel Messi ke da kwallaye 21.

Har yanzu, Mbappe ya zarce Messi da ƙwallo biyu a wannan gasa, inda ya ke da 10, shi kuma Messi ke da 8.
Mbappe shi ne ɗan wasa na farko da ya ci ƙwallaye 10 a Gasar Cin Kofin Duniya ɗaya tun Gerd Muller na Jamus ta Yamma a 1970.

Sai dai a na sa ran kyaftin din Argentina Lionel Messi zai ƙara bayar da mamaki kamar yadda ya saba a wasan ƙarshe da Argentina za ta kece raini da Spaniya ranar Lahadi, 19 ga Yulin 2026.