Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bukaci al’ummomin yankunan dake fuskantar haɗarin ambaliya a faɗin ƙasar nan da su gaggauta canza matsugunni,daidai lokacin da ruwan sama ke ƙara tsananta
Shugabar NEMA, Zubaida Umar, ta bayar da wannan shawara a cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja, wadda Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na hukumar, Malam Manzo Ezekiel, ya rabawa manema labarai.
Darakta Janar ɗin ta ce yawaitar ruwan sama a sassan ƙasar na buƙatar al’ummomi su ɗauki matakan kariya daga ambaliya domin rage illolin da ka iya biyo baya.
- POWA ta bai wa mambobi kayan sana’o’i, ta ƙarfafa su kan kula da lafiya
- Ƙungiyar tsofaffin kansiloli AFFCN da TPI za su wayar da kan al’umma kan gyaran tsarin zaɓe da haraji
- Abuja na samun ci gaba ƙarƙashin Wike shekaru 50 bayan kafuwarta – Tinubu
Ta buƙaci mazauna yankunan da ke cikin haɗarin ambaliya su kula da sanarwar gargaɗi daga hukumomin gwamnati da abin ya shafa, sannan su koma wurare masu tudu idan akwai barazanar ambaliya.
Haka kuma, Zubaida ta shawarci direbobi da masu tafiya a ƙafa da su guji tuƙi ko tafiya ta cikin ruwan ambaliya saboda haɗarin da hakan ke jefa rayuka da dukiyoyi.
Ta kuma gargadi jama’a da kada su riƙa zubar da shara a magudanan ruwa, tana mai cewa toshewar magudanan ruwa na ƙara haɗarin ambaliya.
Darakta Janar ɗin ta bukaci jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani yanayin gaggawa ga hukumomin da abin ya shafa domin damar kai ɗauki cikin lokaci da gudanar da ayyukan ceto.