Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa Freetown, babban birnin ƙasar Saliyo.
Shatima dai zai je Freeetown ne domin wakiltar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatocin ECOWAS karo na 69, wanda za a gudanar a ranar 19 ga Yuli, 2026.
- Ambaliya: NEMA ta bukaci a fara kwashe jama’a yayin da ruwan sama ke ƙaruwa
- Katsewar Wutar Lantarki ta shafi jihohi shida a Arewacin Najeriya – TCN
- Ƙungiyar tsofaffin kansiloli AFFCN da TPI za su wayar da kan al’umma kan gyaran tsarin zaɓe da haraji
Ana sa ran taron zai mayar da hankali kan muhimman batutuwa da suka haɗa da tsaron yankin daa inganta dimokuraɗiyy da kasuwani da bunƙasa ababen more rayuwa da haɓaka tattalin arziki da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen yammacin Afirka.
Shettima zai halarci taron tare da sauran shugabannin ƙasashen yammacin Afirka da manyan jami’an gwamnati, kafin ya dawo Abuja bayan kammala ayyukansa a taron.