Ɗan wasan tsakiya na Faransa, Michael Olise, ya karya tarihin marigayi gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa na Brazil, Pele, na bayar da taimako a zura ƙwallo a Gasar Cin Kofin Duniya daya.
Olise ya samu wannan nasarar ne bayan ya bayar da taimako 2 a wasan neman matsayi na uku da Faransa ta sha kashi da ci 6-4 a hannun Ingila a ranar Asabar.
-
Gasar Cin Kofin Dunuya ta 2026: Ingila ta lashetagulla a kan Faransa
- A karon farko Messi da Yamal sun magantu kan hoton wanka
-
Karambatta tsakanin Joshua da Itauma a Najeriya zai dauki hankalin duniya—Ezekiel Adamu
Taimako biyun da ya bayar ga Les Bleus ya sa ɗan wasan wanda ke taka leda a Bayern Munich ya cika taimako 7 a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026. Hakan ya bashi nasarar karya tarihin Pele da ya bayar da taimako 6 a gasar ta 1970 da aka gudanar a Mexico.

Daga cikin taimako 7 na Olise, 5 kai tsaye ga abokin wasansa Kylian Mbappe ne. Wannan shi ne mafi yawan taimako daga ɗan wasa daya zuwa wani a tarihin gasar. Sai dai ɗan wasan Bayern Munich ɗin bai ci ƙwallo ko ɗaya ba a duk tsawon Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.
