Tawagar sojojin ƙasar Mali da ke kan hanyarta daga garin Anefis mai muhimmanci zuwa Gao ta fuskanci harin kwanton ɓauna da ‘yan tawayen Tuareg suka kai a safiyar Asabar, a cewar jami’an soji da na tsaro.

Majiyoyin soji sun ce harin ya faru ne a kusa da Tabankort, inda aka buɗe wa tawagar wuta yayin da take barin Anefis.

Wata majiya daga ƙungiyar ‘yan tawayen Front de Libération de l’Azawad (FLA) ita ma ta tabbatar da faruwar harin.

Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya ce sojojin Mali sun yi asara mai yawa, duk da cewa wani ɓangare na tawagar ya samu damar ci gaba da tafiya.

Hotunan da ƙungiyar FLA ta fitar sun nuna abin da ta ce su ne sojojin Mali da dama da ta kama a matsayin fursunoni.

A ranar 4 ga Yuli, mayaƙan ƙungiyar FLA tare da mayaƙan ƙungiyar JNIM, mai alaƙa da Al-Qaeda, sun kwace garin Anefis na ɗan lokaci. Wannan na daga cikin jerin hare-haren haɗin gwiwa da ake kai wa a ƙasar Mali cikin ‘yan kwanakin nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *