Kyalian Mbappe, Dan wasan gaba na Faransa da Real Madrid.

A halin yanzu, Kylian Mbappe ne ke jagorantar jerin sunayen ‘yan wasan da ke takarar lashe Takalmin Zinare na wanda ya fi zura yawan ƙwallaye a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.

Mbappe ya na da ƙwallaye 10 a gasar, inda ya zarce Lionel Messi da ƙwallo 2, wanda zai buga wasan ƙarshe ranar Lahadi.

Ƙwallo 2 da Mbappe ya ci a wasan da Faransa ta sha kashi 6-4 a hannun Ingila a wasan neman matsayi na uku ne suka sa ya ƙara tazararsa. Yanzu haka shi ne wanda ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin kofin duniya baki ɗaya da ƙwallaye 22.

Messi, wanda ke da ƙwallaye 8, zai buƙaci ya ci ƙwallo 2 a wasan ƙarshe da Spaniya a ranar Lahadi domin ya zarce Mbappe.

Sai dai Mbappe da Messi sun yi canjaras a ɓangaren bayar da taimako inda kowannen su ke da 4, kuma a na amfani da hakan wajen tantance wa zai lashe Takalmin Zinaren idan sun kammala da yawan ƙwallaye iri ɗaya.

Erling Haaland da Jude Bellingham da aka fitar a gasar suna da ƙwallaye 7, yayin da Harry Kane ke da 6.

Ga manyan ‘yan wasanni 5 na farko da ke takarar lashe Takalmin Zinare na Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026:

 

Matsayi Dan Wasa Ƙasa ƙwallaye
1 Kylian Mbappe Faransa 10
2 Lionel Messi Argentina 8
3 Erling Haaland Norway 7
4 Jude Bellingham Ingila 7
5 Harry Kane Ingila 6

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *