Andy Burnham ya zama sabon Firaiministan Birtaniya bayan ganawa da Sarki Charles III a Fadar Buckingham a ranar Litinin.
Burnham ya ce yana da burin kawo karshen rudanin siyasa da ya dabaibaye kasar a shekaru 10, bayan ganarwar sa da Sarli Charles, inda ya buƙace shi da ya kafa sabuwar gwamnati.
Burnham, ɗan shekaru 56, shi ne Firaiminista na 6 da ya shiga Downing Street a cikin shekaru 10.
Tawagar Burnham ta ce sabon Firaiministan zai bayyana manyan abubuwan da zai baiwa fifiko ta fuskar tsare-tsaren sa ga ƙasar, yayin jawabin sa na farko.
-
Shugaban São Tomé na fuskantar ƙalubale daga ɗan jam’iyyarsa a zaɓen shugaban ƙasa
-
Kotun ECOWAS ta bunkasa hanyoyin samun adalci tare da kaddamar da tsarin gudanar da sharia ta yanar gizo (ECMS)

Har ila yau, Sarki Charles ya gana da tsohon firaiminista Starmer domin karɓar murabus ɗinsa.
Starmer ya bar Downing Street da safiyar ranar Litinin.
A jawabinsa na bankwana, Starmer yace shekaru 2 da ya yi akan mulki Birtaniya ta zama ƙasa mafi kyau da tsari.
“Ina da ƙwarin gwiwa cewa a yanzu Birtaniya ta kasance mafi tsari da kuma adalci fiye da shekaru 2 da suka gabata,”-
“Zan tafi da kyakkyawar niyya, zan tafi da murmushi, kuma zan tafi ina alfahari da duk abin da muka iya cimma,” in ji Starmer.
