Jakadan Najeriya a ƙasar Sin, Ambasada Abdulrahman Danbazau, ya yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar Najeriya da Sin wajen ƙera batirin lithium, inda ya buƙaci masu zuba jari na ƙasar Sin su wuce matakin sarrafa ma’adanai kawai zuwa kafa masana’antun ƙera batir a Najeriya.
Danbazau ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a yayin Taron Horas da Manyan Kafafen Yaɗa Labarai na Afirka da Sashen Hulɗa na Ƙasa da Ƙasa na Jam’iyyar Kwaminis ta Sin ya shirya a birnin Beijing.
Jakadan ya ce yalwar ma’adanai masu muhimmanci da Najeriya ke da su, ciki har da lithium, na ba ƙasar damar sauyawa daga mai fitar da albarkatun ƙasa zuwa cibiyar masana’antu.
- Ana fargabar mutum 40 sun mutu bayan kwalekwale ya kife a Jigawa
- Tsawa ta halaka yara, ta jikkata 2 a Adamawa
- Dillalan mai sun ce shigo da fetur daga waje ya fi na cikin gida tsada
Ya ce Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen tabbatar da cewa Najeriya ta fi cin moriyar albarkatun ƙasarta ta hanyar sarrafa su da kuma ƙera kayayyaki a cikin gida.
Danbazau ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya na ƙarfafa kamfanonin Sin da ke aiki a ƙasar su faɗaɗa ayyukansu daga sarrafa ma’adanai kawai zuwa ƙera kayayyakin da aka gama, musamman batirin lithium.
Danbazau ya ƙara da cewa Najeriya na neman ƙara cin gajiyar dangantakarta da Sin ta hanyar haɓaka haɗin gwiwa a muhimman fannoni kamar masana’antu, noma, kiwon lafiya, kimiyya da fasaha.
Jakadan ya ce Najeriya za ta ci gaba da tattaunawa da masu zuba jari da sauran masu ruwa da tsaki na ƙasar Sin domin tallafa wa sauyin tattalin arzikin ƙasar da kuma ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu.