Ana ci gaba da gudanar da aikin ceto a Jihar Jigawa bayan wani kwalekwale da ke ɗauke da mata da ɗaliban makarantar firamare ya kife a Ƙaramar Hukumar Ringim.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA) ta bayyana cewa mutum aƙalla 40 sun rasa rayukansu a hatsarin.
Sai dai rundunar ‘yan sanda ta ce ya zuwa yanzu an gano gawa guda ɗaya kacal, yayin da jami’an ceto ke ci gaba da neman sauran waɗanda hatsarin ya rutsa da su.
- Dillalan mai sun ce shigo da fetur daga waje ya fi na cikin gida tsada
- Tsawa ta halaka yara, ta jikkata 2 a Adamawa
- Ba ta’addaci ne babbar barazanar Najeriya ba – Kuku
Daraktan Tsare-tsare na Hukumar SEMA ta Jigawa, Muhammad Bala Sanusi, ya ce ana ci gaba da aikin ceto, tare da alƙawarin fitar da ƙarin bayani yayin da aikin ke gudana.
Rahotanni sun nuna cewa waɗanda hatsarin ya rutsa da su na kan hanyarsu ta komawa gida ne bayan tashi daga makaranta lokacin da kwalekwalen ya kife.
A yankuna da dama na Arewacin Najeriya, musamman a lokacin damina, koguna su ne babbar hanyar sufuri ga al’ummomi da dama.
Sai dai yawaitar haɗurran kwalekwale na ci gaba da bayyana haɗarin cunkoso da loda fasinjoji fiye da ƙima, rashin bin ƙa’idojin tsaro, da kuma rashin amfani da rigunan kariya na ruwa (life jackets).