Ƙungiyar Dillalan Man Fetur ta Ƙasa (IPMAN) ta ce shigo da fetur daga ƙasashen waje na ƙara tsadar mai da matsa lamba kan darajar naira. Ta kuma bukaci Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Najeriya, NMDPRA da ta sake duba lasisin shigo da mai domin ƙarfafa tace mai a cikin gida.
Sakataren Yaɗa Labarai na IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce wasu kamfanonin da aka ba lasisin shigo da mai na sayar da man fetur kan kusan N1,350 kan kowace lita, wanda ya ce ya fi farashin da Matatar Dangote ke sayar wa masu kasuwa.
A nata ɓangaren, Ƙungiyar Manyan Masu Kasuwancin Makamashi ta Najeriya (MEMAN) ta ce kuɗin saukar da fetur da aka shigo da shi ya kai N1,190.96 kan kowace lita a ranar 16 ga Yuli. Ta kuma ce matsaikaicin farashin kwanaki bakwai ya kai N1,155.45 kan lita.
- Dillalan Man Fetur sun yi barazanar rufe gidajen mai idan…
-
IPMAN: Sayen fetur kai tsaye daga matatar Ɗangote zai rage farashin lita a gidajen mai
-
FCCPC ga ’yan kasuwa: Ku sauƙaƙe farashin man fetur ko ku fuskanci takunkumi
MEMAN ta danganta hauhawar farashin da raunin naira da kuma tashin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya. Ta ce waɗannan abubuwa ne suka ƙara tsadar shigo da fetur zuwa Najeriya.
IPMAN ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙara tallafa wa Matatar Dangote da sauran matatun cikin gida. Ta ce hakan zai rage dogaro da shigo da fetur daga waje tare da tabbatar da wadataccen mai a ƙasar.
Ukadike ya ce ƙarfafa tace mai a cikin gida zai taimaka wajen daidaita farashin man fetur, kare darajar naira da kuma bai wa Najeriya damar samun ƙarin kuɗaɗen shiga ta hanyar fitar da tataccen mai zuwa ƙasashen waje.
