Ƙungiyar Masu Zaman Kansu ta Dillalan Man Fetur a Najeriya (IPMAN) ta ce ana sa ran farashin litar fetur zai ƙara raguwa idan mambobinta suka fara sayen man kai tsaye daga matatar Dangote.

Shugaban ƙungiyar, Elijah Shettima, ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).

Shettima ya ce babban burin IPMAN shi ne tabbatar da cewa dillalan man fetur masu zaman kansu sun samu damar sayen kayayyakin mai kai tsaye daga matatar Dangote.

A cewarsa, hakan zai inganta wadatar man fetur a kasuwa tare da ƙarfafa gasa, lamarin da zai taimaka wajen rage farashin da masu amfani ke biya.

Ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya ta ci gaba da tallafa wa tace mai a cikin gida ta hanyar samar da yanayin da zai bai wa matatun mai damar gudanar da ayyukansu cikin sauƙi.

Haka kuma ya ce idan buƙatar shigo da mai ta taso, ya kamata a bai wa dillalan masu zaman kansu damar yin hakan kai tsaye.

Shugaban na IPMAN ya bayyana cewa tuni dillalan masu zaman kansu suka rage farashin fetur da kusan naira 125 kan kowace lita a sassan ƙasar, yana mai cewa za su ci gaba da rage farashin idan kuɗin sayen mai daga ma’ajiyun ajiya ya ci gaba da sauka.

Ya ƙara da cewa farashin lita zai ci gaba da sauyawa gwargwadon yanayin kasuwa.

Game da yiwuwar farashin litar fetur ya sauka zuwa naira 900 ko ƙasa da haka, Shettima ya ce hakan zai dogara ne da farashin da dillalai ke sayen mai.

Ya bayyana matakin matatar Dangote na sayar wa dillalan masu zaman kansu kai tsaye a matsayin wani gagarumin ci gaba ga ɓangaren rarraba man fetur, yana mai cewa hakan zai rage kuɗin rabon mai tare da amfani ga masu saye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *