Ƴan siyasa sun fara martani game da kalaman IMF cewa gwamnatin Najeriya ta kashe kuɗaɗen da suka kai kusan kashi biyu cikin ɗari na jimillar arziƙin ƙasar.
Wakilin IMF Christian Ebeke ne ya bayyana hakan a Jihar Legas, cewa ƙasar na kashe kuɗaɗe ba tare da bin ƙa’idar dake ƙunshe cikin bayanan kuɗaɗen gwamnati ba.
A cewarsa, yawancin kuɗaɗen sun shafi manyan ayyukan gwamnati da aka gudanar ta hanyoyin da ba su bi tsarin kasafin kuɗi na yau da kullum ba.
Ya ƙara da cewa hakan na kawo cikas wajen tantance yadda aka kashe kuɗaɗen gwamnati, tare da rage bayyana gaskiya a harkokin tafiyar da kuɗaɗen ƙasa.
Sai dai bayanan na IMF sun haifar da martani daga jam’iyyun adawa, inda tsohon mataimakin shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya buƙaci majalisar dokoki ta Ƙasa da ofishin babban mai binciken kuɗaɗen Gwamnati da kuma hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa su gudanar da cikakken bincike.
