Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya sake jaddada ƙudirin Najeriya na ci gaba da jagorantar ƙoƙarin tabbatar da tsaro da ɗorewar dimokuraɗiyya a yankin Yammacin Afirka.
Cikin wata sanarwa da muƙaddashin jami’in hudda da jama’a na rundunar Appolonia Anele ya fitar, yace Babban hafsan ya bayyana hakane bayan ganawa da Babban Hafsan Rundunar Sojin Guinea-Bissau, Manjo Janar Tomas Djass
Ganawar ta gudana ne a birnin Fatakwal, na Najeriya, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen bikin cika shekaru 163 da kafuwar Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya (NADCEL 2026).
- Sojoji sun ceto mutane 6 daga hannun ‘yan bindiga a Borno
- ‘Yan Sanda sun ceto mata da ɗanta da masu garkuwa suka sace a Jihar Kwara
- Masu bauta da aka sace a Ekiti sun shaƙi iskar ‘yanci
A yayin tattaunawar, Laftanar Janar Shaibu ya bayyana cewa ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin rundunonin sojin ƙasashen Yammacin Afirka na da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin tsaro da ke ƙara ƙamari a yankin, musamman waɗanda ke ketare iyakokin ƙasashe.
Ya ce Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da ta’addanci da ayyukan wanzar da zaman lafiya da kuma kare tsarin dimokuraɗiyya ta hanyar gudanar da ayyukanta cikin bin doka da kyakkyawar hulɗa da fararen hula.
Babban Hafsan ya ƙara da cewa ƙwarewar da Najeriya ta samu a fannin yaƙi da ta’addanci da ayyukan haɗin gwiwar ƙasashe daban-daban ta sanya ta zama ginshiƙi wajen ƙarfafa tsaro a Yammacin Afirka.
A nasa ɓangaren, Babban Hafsan Rundunar Sojin Guinea-Bissau, Manjo Janar Tomas Djass, ya yaba da ƙwarewa da jagorancin Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Ya bayyana aniyar ƙasarsa ta ƙara faɗaɗa haɗin gwiwa da Najeriya ta hanyar musayar ƙwarewa da horaswa da aiwatar da shirye-shiryen haɗin gwiwa domin ƙarfafa ƙarfin rundunonin sojin ƙasashen biyu.
Ganawar ta nuna ƙudirin Najeriya na ci gaba da ƙarfafa alaƙar tsaro da ƙasashen maƙwabta tare da bunƙasa haɗin gwiwar da za ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro da ɗorewar dimokuraɗiyya a faɗin yankin Yammacin Afirka.