Real Madrid ta sayi ɗan wasan baya ɓangaren dama daga ƙungiyar Inter Milan ta ƙasar Italiya, Denzel Dumfries, kan Kuɗi Yuro Milan 20.
A halin yanzu, Dumfries shine ɗan wasa na huɗu da Madrid ta saye gabannin fara kakar gasar La Liga ta bana ta 2026-27, bayan zuwan Bernardo Silva, Ibrahima Konate da Marc Cucurella.
Dumfries wanda ke da yarjejeniyar iya tafiya wata kungiya da Nerazzurri, ƙungiyar da ya koma mata daga PSV a 2021, ya taimaka musu lashe gasar Serie A sau 2 da kofin Coppa Italia sau 3.
-
Gasar Cin Kofin Duniya ta U17 na mata: Flamingos ta doke Benin
-
Faransa ta fitar da Paraguay, za ta sake haduwa da Moroko a Gasar Cin Kofin Duniya
-
Moroko ta cire mai masaukin baƙi Canada daga gasar Cin Kofin Duniya
Kazalika, ya kuma taimaka wa Inter kai wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai sau 2 a lokacin da yake Italiya, amma duka sun ƙare da shan kaye a hannun Manchester City a 2023 da Paris Saint-Germain a 2025.
A jimillance, ya buga wasanni 207 ma kungiyar Inter Milan, inda ya zura kwallaye 27 ya kuma bayar da taimakon zura wasu ƙwallaye 22.
Shi ne ɗan wasa na huɗu da Madrid suka saya a wannan lokacin hutu, yayin da suke shirin fara kakar su ta farko ƙarƙashin Jose Mourinho.
