Kyaftin Harmony Chidi ta wuce Auriane Titibi ta Benin yayin wasan ranar Asabar

A ranar Asabar, tawagar ‘yan matan Najeriya ‘yan ƙasa da shekaru 17, Flamingos, sun doke takwararsu ta Jamhuriyar Benin, Amazons, da ci 3-2 a wasan farko na zagayen ƙarshe na neman tikitin zuwa Gasar Cin Kofin Duniya ta ‘yan kasa da shekaru 17 ta mata na bana.

Wasan, wanda suka buga a filin wasa na Remo Stars da ke Ikenne-Remo, tawagogin biyu sun nuna ƙwarewa da kuma ƙwazonsu wajen neman tikitin don wakiltar ƙasashen su a Gasar Duniya.

Za a buga wasa na biyu na zagayen ƙarshen ne a filin wasa na Stade Kegue da ke Lome, kasar Togo a ranar Asabar mai zuwa, yayin da duk wacce ta yi nasara za ta samu tikitin zuwa Gasar Cin Kofin Duniya ta ‘yan ƙasa da shekaru 17 ta mata ta bana wadda za a gudanar a Moroko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *