‘Ya’ya maza uku na marigayi jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, sun gudanar da addu’a a gefen akwatin gawarsa tare da na wasu ‘yan uwansa huɗu a ranar Lahadi.
Sai dai Mojtaba Khamenei, ɗan da ya gaje shi a matsayin Jagoran Ƙoli na Iran, bai bayyana a wajen taron ba.
Gidan Talabijin na ƙasar Iran ya nuna Mostafa, Meysam da Masoud Khamenei suna addu’a a bayan akwatunan gawar da aka jera a babban filin Imam Khomeini Grand Mosalla da ke Tehran, wani katafaren cibiyar ibada.
- Iran na nuna saƙon ci gaba da ramuwar gayya a taron bankwana da Khamenei
- Ukraine ta kai hare-hare kan cibiyoyin Mai da soji kusa da St. Petersburg A Rasha
- Masu wanzar da zaman lafiya a Somaliya na fuskantar barazana bayan Amurka ta yanke tallafi
An kashe mahaifinsu tare da wasu daga cikin ‘yan uwansu ne a wani harin sama lokacin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da yaƙi kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu.
Yaƙin, wanda ya ɗauki makonni kafin a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, ya haddasa asarar rayuka da ɓarna a faɗin yankin. Duk da haka, gwamnatin addinin Iran mai samun goyon bayan rundunar Islamic Revolutionary Guards Corps (IRGC) ta ci gaba da riƙe mulki.
Domin nuna girmamawa ga gwamnati da juyin juya halin Musulunci, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta shirya mako guda na jana’izar marigayi Khamenei, ciki har da kai gawarsa zuwa wuraren ibadar mabiya Shi’a da ke maƙwabciyar ƙasar Iraki.
Bayan gawar ta kwana ɗaya a cikin zauren girmamawa domin manyan jami’an Iran da baƙi daga ƙasashen waje su yi mata bankwana, an fito da akwatin gawar a ranar Asabar a waje cikin akwatin gilashi. Haka kuma an nuna akwatunan gawar ‘yarsa da surukinsa da matar ɗansa da jikarsa mai watanni 14.
A ranar yau Lahadi, dubban mutane da suka haɗa da sojoji, ɗaliban makarantun addini da sauran jama’a sun cika harabar Mosalla domin yi wa Khamenei da iyalansa bankwana. Wasu daga cikinsu na daga tutoci masu ɗauke da saƙonnin ɗaukar fansa kan Amurka da Isra’ila
Sauran mahalarta taron sun gudanar da addu’o’i tare a cibiyar da aka sanya wa suna na jagoran farko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Ruhollah Khomeini, wanda Khamenei ya gaje shi a shekarar 1989.
Dubban Iraniyawa, da dama daga cikinsu suna kuka yayin da wasu ke dukan ƙirjinsu cikin jimami, sun mamaye harabar Mosalla tun daga daren Asabar zuwa safiyar Lahadi.
A ranar Litinin 6/7/2026 za a gudanar da babban jerin gwanon jana’iza a tsakiyar Tehran, kafin a kai gawar zuwa birnin Qom, cibiyar manyan malamai na Shi’a a Iran, domin ci gaba da bukukuwan jana’iza a ranar Talata.
Daga nan za a kai gawar zuwa ƙasar Iraki domin gudanar da bukukuwa a biranen Najaf da Karbala, masu tsarki ga mabiya Shi’a, a ranar Laraba.
Bayan haka za a dawo da gawar Iran a ranar Alhamis, inda za a yi wani jerin gwanon jana’iza a birnin Mashhad, kafin a binne ta kusa da ƙabarin ɗaya daga cikin manyan limaman Shi’a na tarihi.