Masu bauta 14 da aka sace a majami’ar Christ Apostolic Church a Eda Oniyo-Ekiti, dake ƙaramar hukumar Ilejemeje ta Jihar Ekiti, sun sake shaƙar iskar ‘yanci bayan watanni biyu a hannun masu garkuwa da mutane.

Masani kan harkokin tsaro kuma ƙwararre kan yaki da ta’addanci, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan, inda ya ce an sake waɗanda aka sace da misalin ƙarfe 12 na daren ranar Juma’a, 3 ga watan Yuli, 2026.

A cewar rahoton, an kai waɗanda aka sake zuwa asibiti inda ake duba lafiyarsu da kuma karɓar magani biyo bayan abin da suka fuskanta.

Makama ya ce daga cikin masu bautar su 15 da aka sace a lokacin harin, ɗaya ya rasu a hannun masu garkuwar, yayin da sauran 14 da aka sake suna cikin mawuyacin halin kiwon lafiya.

An sace waɗanda abin ya shafa ne a ranar 28 ga watan Afrilu, 2026.

Ɗaya daga cikin masu bautar 15 da aka sace ya rasu yana hannun masu garkuwa. Sauran wadanda aka sace suna cikin mawuyacin hali ta fuskar jiki da ta hankali bayan abin da suka fuskanta,” in ji Makama.

Izuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto, hukumomi ba su fitar da wata sanarwa ba kan yadda aka sake waɗanda aka sace ko kuma wadanda ke da hannu a harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *