Neymar, byan shan kaye a hannun Norway

Neymar ya sanar da yin murabus daga kwallon kafa ta kasa, bayan da Brazil ta sha kaye da ci 2-1 a hannun Norway wanda ya sa ta fice daga zagaye na 16 na Gasar Cin Kofin Duniya.

Kwallaye biyu na dan wasa Erling Haaland ne suka kawo karshen duk wani buri na sake lashe Kofin Duniya karo na Shida, da Brazil ke fatan zai zame mata babban tarihi.

Tsohon dan wasan Barcelona da Paris Saint-Germain ya shigo filin wasa da mintuna 25 suka rage amma duk da bugun fenareti a karshen wasan, bai iya ceto tawagar sa daga ficewa ba.

Yanzu Neymar zai kammala rayuwarsa ta kwallon kafa ba tare da daukar Kofin Duniya ba ko kuma Ballon d’Or.

Dan wasan na kungiyar Santos, wanda ya yi kuka a filin wasa a karshen wasan, ya shaida wa tashar TV Globo ta Brazil: “Nayi iya abinda zan iya, na yi Iya bakin kokari na-

“Nafara wasa na farko a filin Met life, na kuma kammalla a filin. Yanzu komai yazo karshe.” Inji Neymar.

Martanin Ancelotti

An jiyo Kocin Brazil Carlo Ancelotti na cewa: “Wannan sakamako ne mai matukar takaici kuma dukkanmu muna cikin bakin ciki, amma wannan tawaga ce mai kyau kuma dole in gode wa ‘yan wasana, sun yi aiki tukuru-

“Ban yi tunanin mun cancanci shan kaye ba, amma dole mu yarda da haka. Haka kwallon ƙafa ta gada, wasu lokutan dole ka shawo kan bakin ciki da da shan kaye,” in ji Ancelotti.

Wannan dai shine karo na 6 da tawagar ta so daga kofin duniyar a karo na Shida, sai dai haƙan nasu bai cimma ruwa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *