Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sakkwato ta kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da alburusai.

Kisan, ya biyo bayan daƙile wani hari da aka kai ƙauyen Ɗaraye da ke Ƙaramar Hukumar Wamakko a jihar, kamar yadda Jami’in Hulɗa da Jama’a DSP Ahmad Rufa’i, ya bayyana a ranar Lahadi.

Ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 1:35 na dare, cewa wasu gungun ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari ƙauyen na Ɗaraye.

 

Daga nan ne rundunar ta tura jami’an ta dake sashen yaƙi da  ta’addanci (VCRU), domin ƙarfafar jami’an ta dake yankin Wamako, domin daƙile yunƙurin maharan.

“Jami’an sun yi musayar wuta, kuma sun samu nasarar fatattakar su, lamarin da ya tilasta wa ‘yan bindigar tserewa zuwa cikin daji, kuma ana zargin suna ɗauke da raunukan harbin bindiga.” Inji sanarwar

A yayin binciken da aka gudanar daga baya ne aka gano an kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne, sannan an ƙwato bindiga kirar AK-47 guda ɗaya da kuma harsasai guda 28.

Jihar Sokoto dai tasha fama da hare haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, sai dai hukumomin tsaro a Jihar na cewa suna iya bakin kokarinsu wajen shawo kan lamarin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *