Ministan Bunƙasa Kiwo, Idi Mukhtar Maiha, ya sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya na sauya fasalin fannin kiwo a Najeriya ta hanyar amfani da fasahar zamani da jawo zuba jari da bunƙasa masana’antu da kuma bai wa kamfanoni masu zaman kansu damar jagorantar ci gaban sashen gaba ɗaya.
Maiha ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki da ya kai Jihar Kano, inda ya ƙaddamar da Tsarin Gudanar da Bayanai kan Kiwo na Jihar Kano (Livestock Information Management System – LIMS) a Asibitin Dabbobi na Gwale Model.
Kazalika Ministan ya duba Kamfanin Fatar Dabbobi na KANOTAN S.A.
Ya bayyana tsarin a matsayin abin koyi na yadda za a tafiyar da harkokin kiwo cikin inganci ta amfani da fasahar zamani.
- Tattaunawa tsakanin addinai ce hanyar samun ɗorewar zaman lafiya –Tinubu
- Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da gina wasu hanyoyin naira biliyan 135 a Jihar Borno
- Sojoji sun ceto mutane 6 daga hannun ‘yan bindiga a Borno
Tsarin ya ƙunshi rajistar dabbobi da adana bayanan lafiyar dabbobi da sa ido kan yaɗuwar cututtuka da bibiyar allurar rigakafi da bayar da lasisi da kuma tallafa wa masu kiwo.
Maiha ya ce za a haɗa tsarin da shirin gwamnatin tarayya na ƙasa domin inganta musayar bayanai da tsare-tsare da kuma samar da ingantattun manufofi a fannin kiwo.
Sai a ‘yan shekarun nan sana’ar kiwo ta sha fuskantar kalubale da suka haɗa rikice-rikicen makiyaya da manoma da ƙarancin abinci da ruwa ga dabbobi da yawaitar cututtukan dabbobi da sauyin yanayi da kuma rashin isasshen tallafin gwamnati.