‘Yan takara shida da ke neman zama babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) sun jaddada muhimmancin dawo da martaba da amincewar da ƙungiyar ke da ita, yayin wata muhawara da aka gudanar a birnin New York ranar Alhamis, mako guda kafin fara zaɓen sabon shugaba a hukumance

Yayin da kamfen ɗin neman kujerar bai fito da wani ɗan takara da ya fi sauran karɓuwa ba, masu neman mukamin sun amsa tambayoyi na kusan sa’o’i biyu daga jami’an diflomasiyya, ma’aikatan MDD da wakilan ƙungiyoyin fararen hula a babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya.

An kuma watsa muhawarar kai tsaye ta kafar Bloomberg.

Masu neman kujerar sun haɗa da Michelle Bachelet daga Chile da Maria Fernanda Espinosa daga Ecuador da Rafael Grossi daga Argentina da Rebeca Grynspan daga Costa Rica da Carolyn Rodrigues-Birkett daga Guyana da kuma Macky Sall daga Senegal.

Dukkansu na neman maye gurbin Antonio Guterres, wanda wa’adinsa zai ƙare a ranar 31 ga Disamba 2026.

Kowane ɗan takara ya bayyana dalilan da ya sa yake ganin shi ne ya fi dacewa da shugabancin MDD, yana mai bayyana ƙwarewarsa wajen fuskantar ƙalubalen rikice-rikicen duniya, tare da nuna gogewarsa a matakin ƙasa ko na ƙasa da ƙasa, da kuma ikon tattaunawa da kowane ɓangare.

A ranar 30 ga Yuli, mambobi 15 na Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya zai gudanar da zaɓen farko na sirri, ba tare da bayyana sunayensu ba, domin nuna wanda suka fi so a cikin ‘yan takarar

Bayan wannan zaɓen na farko, wanda ake kira “straw poll”, za su ci gaba da gudanar da irin waɗannan zaɓukan har sai wani ɗan takara ya samu aƙalla ƙuri’u tara da ake buƙata, ba tare da wani daga cikin mambobi biyar na dindindin ya yi amfani da haƙƙinsa na ƙin amincewa (veto) ba. Waɗannan ƙasashen su ne Amurka da Birtaniya da China da Faransa da Rasha.

Daga nan ne za a miƙa sunan ɗan takarar da aka zaɓa ga Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya domin tabbatar da naɗinsa a hukumance. Wanda aka zaɓa zai fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *