Yayin da gobarar daji ke ci gaba da lalata manyan yankuna a yammacin kasar Faran (France) da tsakiyar ƙasar Sifan (Spain), kusan mutane 200,000 ne aka tilasta wa tserewa, sakamakon yadda gobarar ke cin kurmi da gidaje a kusa da Bordeaux da Madrid.
Jami’an kashe gobara sun bayyana cewa gobarar—wadda ita ce mafi girma da aka taba yi a ƙasashen biyu a shekarun baya-bayan nan—ta yi girman da ba za su iya fuskantarta gaba-da-gaba ba.
A gabar tekun Atlantika na kasar Faran, an kwashe mutane 44,000 daga tsibirin Cap Ferret, yawancin su ta hanyar jiragen ruwa.
An kwashe mutane daga garuruwan da ke kusa da Bordeaux, a matsayin “matakin rigakafi” sakamakon yadda mai ƙarfi ke ƙara ruruta wutar zuwa garin.
A safiyar Asabar, hukumomin yankin sun sake ba da umarnin kwashe mutane daga wasu unguwanni uku da ke yammacin birnin “domin tabbatar da tsaron mazauna.”
Gaba ɗaya, hukumomin ƙasar Faran sun ce an kwashe fiye da mutane 140,000 a yankunan Gironde da Landes da ke yammacin ƙasar.
- ‘Yan takara 6 na neman maye gurbin Guterres a Majalisar Ɗinkin Duniya
- Super Falcons za ta fara kare kambunta na WAFCON akan Malawi ranar Lahadi
- Kotu ta dakatar da shirin binciken tsige Shugaba Cyril Ramaphosa
A ƙasar Sifaniya kuma, Ma’aikatar Cikin Gida ta bayyana cewa mutane 60,000 ne aka tilasta wa tserewa.
Hukumomi a Faransa sun ce manyan gobarun guda biyu na ƙasar sun tashi ne ta hanyar tsautsayi, sannan kuma sakamakon yadda lokutan bazara ke ƙara zafi da rashin ruwa, nau’in irin waɗannan gobarun na ƙara girma sosai.
Ministan Cikin Gida na ƙasar Faran, Laurent Nunez, wanda ya ce gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don kare ‘yan ƙasa, ya yi gargadin cewa sauyawar firgita iska ta maida gobarar Cap Ferret zuwa “gobarar da ke cin kanta kuma ke da wahalar gaske a kashe ta.”
“Yanzu haka tana matsawa zuwa gabas, wato bangaren birnin Bordeaux,” in ji Nunez, wanda ya yi alkawarin: “Zamu sake tsara martaninmu ta yadda zamu iya yaki da ita daga kasa kuma mu hana ta karasawa zuwa Bordeaux.”
Shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron ya buƙaci ɗauki daga Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) a ranar Juma’a, gami da tura dakarun sojin Faran domin dakatar da gobarar wadda kawo yanzu ta lalata fili mai girman hekta 22,000 (eka 54,000).
Hukumar Tarayyar Turai ta sanar da cewa tana tura jiragen sama guda uku na kashe gobara zuwa Faransa, sannan guda huɗu zuwa Sifaniya domin samun nasarar shawo kan lamarin.