Ana zargin wasu ‘yan bindiga da sace Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, Hon. Nura Umar Bungudu, bayan sun kai hari gidansa da ke garin Bunguɗu.
Rahotanni sun ce maharan sun kutsa cikin garin ne a daren Alhamis, inda suka nufi gidan shugaban ƙaramar hukumar da ke unguwar Zango, mai nisan kasa da kilomita 20 daga babban birnin jihar, Gusau.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida cewa maharan sun yi galaba a kan jami’an tsaron da ke gadin gidan, inda suka kashe ‘yan sanda biyu da jami’an sa-kai biyu, kafin su tafi da shugaban ƙaramar hukumar tare da wasu daga cikin ‘yan uwansa.
-
Sojojin Operation Haɗin Kai sun cafke masu garkuwa da mutane 5 a Yobe
-
Mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba: Disu ya ba da umurnin fara samamen makonni 2 a Benue.
Majiyar ta ce jami’an tsaron sun yi ƙoƙarin daƙile harin, amma sun kasa shawo kan maharan saboda irin makaman da suke ɗauke da su. Ta kuma zargi masu bai wa ‘yan bindigar bayanan sirri da taka rawa wajen sauƙaƙa musu kai hare-haren da suke yi a yankin.
Mazaunin ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su kara ɗaukar matakan inganta tsaro a Bunguɗu da sauran al’ummomin da ke fuskantar barazanar hare-haren ‘yan bindiga, yana mai cewa mazauna yankin sun haɗa kai da jami’an tsaro wajen kare garin, amma maharan sun fi karfinsu saboda -manyan makamai da suke amfani da su.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba. Kazalika, ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, bai yi nasara ba, domin ba a samu amsa ga kira da saƙon kar-ta-kwana da aka aika masa ba.