Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga likitocin Najeriya da sauran ƙwararrun ma’aikatan lafiya da ke zaune a ƙasashen waje da su dawo gida domin ba da gudummawar ƙwarewarsu wajen inganta tsarin kiwon lafiyar ƙasar a ƙarƙashin Renewed Hope Agenda.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar Kungiyoyin Likitocin ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (Nigerian Diaspora Medical Associations Worldwide), ƙarƙashin jagorancin Babbar Daraktar Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NIDCOM), Hon. Abike Dabiri-Erewa, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a wani ɓangare na bikin Ranar Diaspora ta Ƙasa ta 2026.

Tinubu ya ce Najeriya na buƙatar ilimi da gogewa da ƙwarewar ’yan Najeriya da ke ƙasashen waje domin gina ingantaccen tsarin kiwon lafiya da zai iya biyan buƙatun al’umma.

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na aiwatar da manyan gyare-gyare a fannin lafiya ta hanyar ƙarfafa cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko da faɗaɗa damar samun ingantattun ayyukan lafiya da bunƙasa ilimin likitanci da bincike da amfani da fasahar zamani da kuma samar da manufofin da za su rage ficewar ƙwararru zuwa ƙasashen waje.

Shugaban ya kuma yaba wa likitocin bisa ayyukan jinya da suka gudanar kyauta a yankuna daban-daban na ƙasar, inda suka gudanar da tiyata, duba marasa lafiya, ba da shawarwari kan lafiya da sauran ayyukan ceton rayuka.

Ya buƙaci su ci gaba da zama jakadun Najeriya ta hanyar ƙarfafa sauran ƙwararrun likitocin da ke ƙasashen waje su dawo gida ko kuma su haɗa kai da gwamnati ta hanyar musayar ilimi da saka hannun jari a fannin lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *