Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya (NPF) ta yi karin haske kan wani rahoto da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta, wanda ke ikirarin cewa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Olatunji Rilwan Disu, ya umarci jami’an ‘yan sanda da su harbe duk wanda aka samu da bindiga ba bisa ƙa’ida ba.

A cikin wata sanarwa, rundunar ta bayyana cewa rahoton ƙarya ne, inda ta ce bai nuna ainihin abin da Sufeto Janar ya faɗa ba

Sanarwar ta ce a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Makurdi, babban birnin Jihar Benue, IGP bai bayar da wani umarnin “harbi nan take” ga jami’an ‘yan sanda ba, inda ta ƙara da cewa an cire kalamansa daga mahallinsu tare da fassara su ta hanyar da ba ta dace ba

Rundunar ta bayyana cewa a cikin jawabinsa, Sufeto Janar ya tunatar da jami’an ‘yan sanda cewa jami’an tsaro da doka ta amince da su ne kaɗai ke da hurumin ɗaukar makamai

Haka kuma, ya yi magana kan yadda mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba ke ƙara ta’azzara matsalolin tsaro, inda masu aikata laifuka ke amfani da su wajen garkuwa da mutane, fashi da makami, ta’addanci, rikicin ƙungiyoyin daba da sauran manyan laifuka.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa IGP ya tunatar da jami’an ‘yan sanda cewa amfani da bindiga yana ƙarƙashin tanade-tanaden dokar Force Order 237, wanda ya fayyace yanayi da lokutan da jami’in ɗan sanda zai iya amfani da bindiga bisa doka yayin gudanar da aikinsa

A cewar rundunar, Sufeto Janar ya jaddada cewa dole ne jami’an ‘yan sanda su yi aiki cikin iyakokin doka tare da bin ƙa’idojin da aka tanada kan amfani da ƙarfi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *