Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya buƙaci ma’aikatan hukumar da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da riƙon amana da kuma nuna ƙwazon aiki domin tabbatar da sahihin zaɓe a shekarar 2027.

Amupitan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wata ziyarar aiki da ganawa da shugabanni da ma’aikatan hukumar a hedikwatar INEC ta Jihar Neja da ke Minna.

Ya ce hukumar ba za ta iya gazawa ‘yan Najeriya ba a babban zaɓen shekarar 2027, yana mai gargaɗin ma’aikatan da su guji duk wani nau’in cin hanci ko saɓa wa ƙa’idojin aiki.

A cewarsa, hankalin ‘yan Najeriya da kuma ƙasashen duniya, ciki har da Tarayyar Afirka da ƙungiyoyin sa ido kan zaɓe na ƙasashen waje, ya riga ya karkata kan yadda Najeriya za ta gudanar da zaɓen mai zuwa.

Shugaban na INEC ya tabbatar wa ma’aikatan cewa hukumar na aiki tukuru wajen inganta harkokin sufuri da kayan aiki da sauran abubuwan more rayuwa a ofisoshin jihohi domin kauce wa matsalolin da suka taso a zaɓukan baya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa shugaban INEC din ya kuma ziyarci cibiyar rajistar masu kaɗa ƙuri’a  (CVR) da ke cikin hedikwatar hukumar a Jihar Neja domin duba yadda ake gudanar da aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *