Shugaban Ƙasar Bangladesh, Mohammed Shahabuddin, ya yi murabus daga mukaminsa, yana mai bayyana cewa taɓarɓarewar lafiyarsa ta hana shi ci gaba da gudanar da nauyin da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ɗora masa.

Shahabuddin mai shekaru 76 ya tabbatar da matakin nasa ne a wata tattaunawar wayar tarho, bayan rahotanni sun nuna cewa yana shirin sauka daga mulki kafin wa’adin aikinsa ya ƙare a shekarar 2028.

A cikin wasiƙar murabus da ya aikawa Kakakin Majalisar Dokoki, shugaban ya bayyana cewa lafiyarsa ta jiki da ta ƙwaƙwalwa sun ƙara taɓarɓarewar, lamarin da ya sa ba zai iya ci gaba da gudanar da ayyukan shugaban ƙasa yadda ya kamata ba.

Shahabuddin, wanda aka fi sani da “Chuppu,” Majalisar Dokokin Bangladesh ta zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a shekarar 2023 tare da goyon bayan jam’iyyar Awami League, wacce tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina ke jagoranta

Bayan zanga-zangar ɗalibai da ta tilasta wa Sheikh Hasina barin mulki a shekarar 2024, an fara matsa wa Shahabuddin lamba da ya yi murabus saboda kusancinsa da gwamnatin Hasina.

A farkon wannan shekara, Shahabuddin ya musanta zargin cewa ya tattauna da Sheikh Hasina ta waya yayin da yake jinya a birnin London na Birtaniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *