Mazauna da masu amfani da hanyar Karu a Babban Birnin Tarayya (FCT) sun nuna godiyarsu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Ministan FCT, Nyesom Wike, bisa kammala aikin hanyar mai tsawon kilomita 15.

Sun bayyana cewa wannan ci gaba ya rage cunkoson ababen hawa, ya dakile ambaliyar ruwa, sannan ya inganta harkokin kasuwanci a yankin.

Aikin, wanda aka ba wa kamfanin cikin gida mai suna Abdul-Val Nigeria Limited,  a ranar 22 ga Agusta, 2025, ya taso ne daga Karu da ke kan titin Abuja zuwa Keffi har zuwa Mararrabar Asibitin Kwastam.

Haka zalika, aikin ya haɗa da muhimman hanyoyin cikin gida irin su Hanyar DSS da Hanyar NIA da Hanyar EFCC da Hanyar Asibitin Primus, da Hanyar Tsohon Unguwar Ma’aikatan CBN.

Shekaru da dama, mazauna yankin da masu tuka ababen hawa sun fuskanci matsalar matsatsin cunkoso da karancin magudanar ruwa da kuma ambaliya musamman a lokacin tsakiyar damina.

Tuni mazauna yankin da suka yi magana kan kammala aikin suka ce lamarin ya canza kwarai da aniyya.

Wata mai shago, Mrs. Chinyere Obasi, ta ce inganta hanyar ya yi tasiri mai kyau sosai a kan kasuwancinsu.

“A baya hanyar ba ta da kyau ko kadan. Kuma babu fitilun kan titi. Amma yanzu kamar yadda kuke gani, hanyar ta yi kyau. Kasuwancinmu kuma, cikin ikon Allah, ya fi na baya albarka,” in ji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *