Tsohon Shugaban ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce taimakon da Najeriya ta bai wa Afirika ta Kudu, wajen gwagwarmayar ‘yantar da kai yasa ƙasar ta kawo ƙarshen tsarin wariyar launin fata.
Obasanjo, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin C-Suite Cafe, wanda Ikem Okuhu ke gabatarwa. Ya yi magana ne kan rawar da Najeriya ta taka wajen yaƙi da mulkin tsirarun fararen fata a Afirika ta Kudu da kuma goyon bayan ƙungiyoyin neman ‘yanci a kudancin Afirika.
Afirika ta Kudu, ta gudanar da zaben ta na farko karkashin mulkin dimokuradiyya ba tare da wariyar launin fata ba a shekarar 1994, inda hakan ya kawo ƙarshen mulkin wariyar da ta shafe shekaru tana fuskanta.
Obasanjo, ya ce Najeriya ba ta shiga wannan gwagwarmaya ba domin neman wata riba ta kuɗi ko siyasa ba, sai dai saboda imanin cewa bai kamata a mayar da baƙar fata a matsayin wanda bai da darajar kaman sauran mutane ba.
Tsohon shugaban, ya ce Najeriya da sauran shugabannin Afirika sun yi imanin cewa ’yantar da baƙar fata a Afirika wani nauyi ne da ya rataya a kansu.
Ya bayyana irin wannan matsaya a matsayin abin da ya kamata Najeriya ta yi alfahari da shi, yana mai cewa taimakon da ta bayar ya taimaka matuƙa wajen yaƙi da wariyar launin fata.
Obasanjo, ya kuma ambaci wasu shugabannin Afirika da na ƙasashen duniya da suka taka rawa a wannan gwagwarmaya, ciki har da Julius Nyerere na Tanzania da Kenneth Kaunda na Zambia da Samora Machel na Mozambique.
Ya kuma ambaci tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter da tsohon Firaministan Birtaniya James Callaghan da tsohon Firaministan Sweden Olof Palme.
Sai dai kalaman Obasanjo, sun zo ne a daidai lokacin da dangantakar Najeriya da Afirika ta Kudu ke fuskantar sabbin matsaloli sakamakon hare-haren da ake zargin wasu ‘yan Afirika ta Kudu da kai wa ‘yan Najeriya dake zaune a ƙasar.
A makon da ya gabata ne Majalisar Dokokin Najeriya ta dakatar da ziyarar jami’ai zuwa Afirika ta Kudu tare da umartar a kaurace wa wasu ayyukan majalisa da ƙasar ke ɗaukar nauyinsu ko shirya su.
Obasanjo, ya kuma yi Allah-wadai da hare-haren, yana mai cewa ba za a iya amfani da matsalar shige da fice ba bisa ƙa’ida ko zargin aikata laifuka a matsayin hujjar kai wa baƙin haure hari ba.
Yana mai ra’ayin cewa wasu ‘yan kasashen waje ma suna taimakawa tattalin arzikin Afirika ta Kudu ta hanyar samar da ayyukan yi, don haka bai dace a riƙa ɗaukar dukkan baƙin haure a matsayin masu kwace wa ‘yan ƙasar ayyukan yi ba.