Hare-haren mayakan Houthi daga Yemen sun jikkata fararen hula 13 a Saudiyya, yayin da hukumomi suka bayar da gargadin kai hare-hare a birane da dama a safiyar Talata.
Kungiyar Houthi mai samun goyon bayan Iran ta kai hare-haren makamai masu linzami kan fararen hula a biranen Khamis Mushayt, Abha da Taif, da jirage marasa matuka a ranar Litinin.
- Sudan: Birtaniya ta fara tattauna kan kawo ƙarshen yaƙin basasa
- Dokar haramtawa Yara amfani da kafafen sada zumunta zata fara aiki a Turai
- Indonesia na laluben fasinjoji da suka bace bayan kifewar jirgin ruwa
Kakakin rundunar hadin gwiwa mai yaki da Houthi a Yemen, Manjo Janar Turki Al-Malki, ya ce hare-haren sun jikkata fararen hula 13 da raunuka daga kanana zuwa matsakaita, tare da lalata gidaje bakwai da motoci biyu.
Al-Malki ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a kafafen sada zumunta da sanyin safiyar Talata.
A nata bangaren, Hukumar Kare Fararen Hula ta Saudiyya ta bayar da gargadin kai hare-hare ga mazauna birane da dama a yammaci da kudancin kasar, ciki har da Abha, Jeddah, Jazan, Taif, Yanbu da Al’Ula.
A ranar Juma’a kuma, Saudiyya ta dakatar na wani aikin shimfida bututun mai na dan lokaci a Riyadh da Madina, bayan wasu jerin hare hare.
Mayakan Houthi na matsa kaimin a yankuna da ake hakar danyen mai a kasar Saudiyya, biyo bayan tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu.