Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama mutane 70, bayan wani faifan bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, wanda ke zargin an yi fashi a kusa da wajen shakatawa na Unity Fountain da ke Unguwar Maitama.

Daga cikin mutanen da aka kama, rundunar ta ce an saki 30 bayan tantance su da kuma bin matakan da suka dace, yayin da aka tsare sauran 40 domin ci gaba da bincike.

A yayin binciken, wanda aka bayyana a matsayin wanda lamarin ya shafa ya gane mutane biyu daga cikin waɗanda ake tsare da su, yana mai cewa ya san su daga lokacin da lamarin ya faru.

Rundunar ta ce mutanen biyu da wanda abin ya shafa ya gane, tare da sauran waɗanda ake tsare da su, suna hannun ’yan sanda yayin da bincike ke cigaba da gudana domin gano gaskiyar lamarin.

Lamarin ya biyo bayan wani faifan bidiyo da ke yaduwa a kafafen sada zumunta, wanda ke zargin faruwar fashi da makami a wajen shakatawar na Unity Fountain.

Bayan ganin faifan bidiyon, Kwamishinan ’yan sandan FCT, CP Ahmed Muhammed Sanusi, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken sumame a wuraren da ake zargin an aikata laifin.

An gano cewa anan ne masu aikata laifuka ke fakewa. Rundunar ta buƙaci mazauna Abuja da su kasance masu taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani mutum, motsi ko aiki da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *