Hukumar Gudanarwa ta Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta tabbatar da mutuwar mutane biyu sakamakon ɓullar cutar mashako a babban birnin ƙasar, inda aka samu mutane 5 da gwajin na’ura ya tabbatar suna ɗauke da cutar daga cikin mutane 15 da aka gudanar da bincike a kansu.
Sakataren Hukumar Kula da Ayyukan Kiwon Lafiya da Muhalli ta FCTA, Dr. Adedolapo Fasawe, ita ce ta bayyana hakan a jiya yayin wani taron wayar da kai da wayar da kan al’umma game da cutar a garin Karshi.
Ta bayyana cewa FCTA ta gudanar da bincike kan mutane 15 da ake zargi zuwa makon da ya gabata, inda mutane biyar aka tabbatar suna ɗauke da mashako, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu, yayin da aka sami nasarar yi wa marasa lafiya da dama magani aka kuma sallame su.
Sai dai kuma, Dr Fasawe ta kwantar wa mazauna garin hankali, inda ta ce hukumar ta ɗauki matakan da suka dace don shawo kan cutar da kuma hana ci gaba da yaduwarta.
Ta yi bayanin cewa mashako wata cuta mai tsanani ce ta ƙwayoyin cuta (bakteriya) wadda ke shafar hanci da maƙogwaro sosai, wani lokacin kuma tana iya shafar fatar jiki.
- Hutu da Tutsi: Rwanda ta tuna da waɗanda suka rasu a kisan kiyashin 1994
- Wacce rawa Ƙasar Jordan ke takawa a rikicin Gabas ta Tsakiya
- Barrow ya yi alƙawarin kawo ƙarshen matsalar wutar lantarki
A cewarta, alamomin farko sun haɗa da zazzabi da tari da da majina, wanda zai iya rikiɗewa zuwa kumburin wuya da kuma matsananciyar wahala wajen yin numfashi.
Ta ja kunnen mazauna yankin game da shan magani da kansu da kuma ƙoƙarin cire fure ko tsumman da ke fitowa a saman maƙogwaro na mutanen da suka harbu da cutar.
Dr Fasawe ta tunatar da su wani mummuna al’amari inda aka ruwaito cewa wani yaro ya zubar da jini har ya mutu bayan da wani mai aski na gargajiya ya yi ƙoƙarin yanke wannan fure na maƙogwaro, tana mai kiran mazauna yankin da su hanzarta rahoton mutanen da ake zargi zuwa ga hukumomin kiwon lafiya na gwamnati.
Don shawo kan wannan ɓullar cutar, ta ce FCTA ta tura tawagar ƙwararru ta gudanar da al’amuran gaggawa (Incident Management Team) zuwa Karshi da sauran ƙauyuka da biranen da ke makwabtaka da su don gano mutanen da aka yi hulɗa da su, da ba da magungunan rigakafi, da kuma ƙarfafa wayar da kan al’umma a harsunan gida, ciki har da Hausa da Gbagyi.
Sarkin Karshi, Ismaila Mohammed, wanda shugaban ƙaramar hukuma, Alhaji Ahmed Doka ya wakilta, ya bayyana cewa mutuwar da aka samu ba a cikin garin Karshi ta faru ba, a wani matsuguni ne da ke kan iyaka da Jihar Nasarawa.
Ya nuna godiyarsa ga saurin shiga tsakani na gwamnati kuma ya yi alƙawarin goyon bayan shugabannin gargajiya da na addini wajen tabbatar da cewa mazauna yankin sun kai yara marasa lafiya zuwa cibiyoyin kiwon lafiya da aka ware maimakon neman magungunan gargajiya marasa inganci.
Ita ma da take jawabi, Hanatu Bello, wadda ta wakilci Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya (NCDC), ta tabbatar wa mazauna yankin cewa hukumar tana ba da dukkan tallafin fasaha da gudanarwa ga FCT don dakatar da yaɗuwar cutar da kuma ƙarfafa hanyoyin sadarwa na kiyaye haɗari.
Jami’ar kula da FCT ta Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Imaobong Adebayo, wadda Dr. Jibril Alkasim ya wakilta, ta jaddada wadatar da kuma amincin rigakafin eka na gabaɗaya kyauta ga yara.