Kasar China ta bukaci Amurka ta jingine shirin ta na ajiye makamai a duniyar wata, bayan da babbar cibiyar rundunar tsaron sararin samaniya ta Amurka (U.S. Space Force) ta tabbatar da cewa a karon farko ta girke makamai a sararin samaniya.
Ma’aikatar Harkokin Wajen China ta yi adawa da matakin, tana gargadin illar mayar da samaniya wurin ajiyar makamai, sauya shi zuwa fagen daga, da kuma fara gasar tara makamai a sararin samaniya
Da yake Magana a wani taron manema labarai, Kakakin ma’aikatar wajen kasar Sin, Guo Jiakun, ya ce “Muna kira ga kasar Amurka da ta kaucewa kokarin ta n mayar da sararin samaniya fagen daga.”
- Wasu Hare-haren sun jikkata fararen hula 13 a Saudiyya
- Sudan: Birtaniya ta fara tattauna kan kawo ƙarshen yaƙin basasa
- Dokar haramtawa Yara amfani da kafafen sada zumunta zata fara aiki a Turai
A sanarwar da ta fitar, cibiyar rundunar tsaron sararin samaniya ta Amurka ta ambaci China da Rasha a matsayin wata barazana, tana cewa Beijing da Moscow “na kerawa tare da amfani da dabarun sarrafa sararin samaniya da na hana abokan gaba amfani da shi, a matsayin wani bangare na dabarun zamanantar da ayyukan soji.”
Aikin mayar da sararin samaniya wani bangare na ayyukan soji, ya samo asali ne tun farkon da kasashe suka fara gasar zuwa duniyar wata, bayan da Tarayyar Soviet ta harba tauraron dan Adam na farko mai suna Sputnik, a shekarar 1957.
Washington da Moscow, sun fara neman hanyoyin da za su iya amfani da makamai wajen kare ko lalata irin wadannan tauraron dan adam da ake harbawa, kafin daga bisani su yi kaka gida a cikin harkar.