Cibiyar ‘Yan Jarida Masu Fafutukar Zaman Lafiya (Network of Peace Journalists – NPJ) ta jinjina wa Ofishin Jakadancin Jamus da ke Najeriya, Cibiyar Shiga Tsakani ta Addinai (Interfaith Mediation Centre – IMC), da kuma Kotun Koli ta sasanci ta Jihar Kaduna (Kaduna State Multi-Door Courthouse – KDMDC)

Yabon na zuwa ne a sakamakon shirya wani taron bita na kwanaki biyu, kan tsarin magance rikice-rikice tsakanin al’umma ba tare da daukaka matsalar zuwa ga kotu ba, wanda sama da masu ruwa da tsaki 60 daga sassan Jihar Kaduna suka halarta.

Shugaban Kungiyar NPJ, Ambasada Ibrahima Yakubu, ne ya bayyana wannan yabo a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai bayan kammala taron bitar na kwanaki biyu.

Ya bayyana shirin a matsayin wani mataki da nufin karfafa gwiwa da kwarewar masu ruwa da tsaki wajen kiyaye aukuwar rikici, sasanci da shiga tsakani idan wani sabani ya auku, domin inganta zaman tare a cikin al’umma.

A cewarsa, taron ya samu mahalarta daga bangaren ma’aikatan shari’a, masana a fannin doka, kungiyoyin farar hula, masana kimiyya, shugabannin mata da na bangaren addinai daga shiyyoyi uku na Jihar Kaduna.

Haka nan, mahalartan sun hada da wakilai daga Hukumar Karbar Korafe-Korafen Jama’a (PCC), Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Kasa da Kasa (IHRC) da malaman jami’a.

Ambasada Yakubu ya bayyana cewa taron bitar ya fahimtar da mahalarta taron hanyoyin da suka dace na fahimtar yadda rikici ke faruwa, binciken musabbabin rikici, nau’ikan halayen mutane, da kuma hanyoyin magance rikici ta hanyar ADR (wato sasanci ba tare da an je kotu ba).

Ya lura cewa ilimi da kwarewar da aka samu a lokacin shirin zai ba mahalarta damar tsoma baki cikin magance takaddamar a tsakanin al’umma, da kuma hana karamin sabani ko fitina rikidewa zuwa babba.

Ya kara bayyana cewa an karfafawa mahalartan gwiwa wajen kafa abin da ya kira “zauren sasanci” (mediation tents) a cikin al’ummominsu da wuraren ayyukansu, inda za a rika magance takaddama ta hanyar tattaunawa da sanya baki kafin abubuwa su kai ga matakin shari’a a kotu.

Ambasada Yakubu ya kuma yaba wa Ofishin Jakadancin Jamus da Cibiyar IMC saboda ci gaba da ba da tallafi ga ayyukan wanzar da zaman lafiya, musamman shirye-shiryen da ke inganta halartar mata wajen samar da zaman lafiya, kare hakkin dan adam, da ‘yancin zabar addini.

Ya jaddada cewa zuba jari a fannin shiga tsakani, tattaunawa, da kuma hada karfi da karfe wajen samar da daidaito zai taimaka wajen gina al’ummomi nagartacciya, da kuma bayar da gudunmawa ga dorewar zaman lafiya da ci gaba a Jihar Kaduna da ma Najeriya baki daya.


 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *