Shugaban jam’iyyar Green Party ta Birtaniya, Zack Polanski, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar neman kujerar Majalisar Dokokin Birtaniya, da tsohon Firaministan kasar Keir Starmer, ya bari bayan ya yi murabus.
Polanski ya tabbatar wa jaridar Camden New Journal cewa shi ne dan takarar jam’iyyar Green Party a mazabar Holborn da St Pancras, wadda ke karkata ga yan gurguzu a siyasar kasar.
Polanski ya ce: “Na shafe shekaru da dama ina rayuwa da kuma aiki a wannan al’umma, na san ta sosai, kuma ina sonta.”
- Yadda ƙungiyoyin fararen hula suka gudanar da gangamin goyon bayan janar Tiani
- Iran ta ce hare-haren Amurka sun kashe mutane huɗu a wajen bikin aure
- Jamus zata rufe ofishin jakadancin Rasha dake Bonn
Ya kara da cewa: “Tana kunshe da abubuwa da dama da suka sa Landan ta kasance birni na musamman, kuma Ina matukar farin ciki da yiwuwar wakiltar wannan wuri a Majalisar Dokoki.”
Sanarwar Polanski ta zo ne kwanaki kadan bayan tsohon Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya bayyana cewa zai sauka daga mukaminsa na dan Majalisar Dokoki, lamarin da ya jawo bukatar gudanar da zaben cike gurbi.
Starmer ya bayyana ranar Talata cewa lokaci ya yi da zai yi murabus daga kujerar dan Majalisar Dokoki mai wakiltar Holborn da St Pancras, bayan shafe shekaru 11 yana wakiltar mazabun.
Wannan sanarwa ta zo ne makonni shida, bayan ya yi murabus daga mukaminsa na Firaiministan Birtaniya, bayan ya rasa goyon bayan ‘yan majalisar jam’iyyarsa ta Labour mai mulki.