Darakta Janar na Hukumar tsaro na farin kaya (DSS), Oluwatosin Ajayi, ya umarci jami’ansa da kada su sake kama kowa a kan takaddama dake tsakanin farar hula.

Ajayi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar Alhamis a Abuja.

Na shaida wa abokan aiki na cewa kada a sake kama kowa a kan al’amuran da suka shafi jama’a, kuma na tabbata kun ankare cewa, ko a shari’o’in da suka shafi yan jarida, mun gwammace mu tafi kotu saboda aiki guda muke yi

A cewarsa, wannan umarni na daga cikin ƙoƙarin inganta bin tsari na doka da oda, da kyautata tarihin hukumar wajen kare haƙƙin ɗan adam.

Ajayi, ya bayyana cewa tun lokacin da ya kama aiki, ya aiwatar da sauye-sauye guda biyar. Sune aiwatar da doka, haɗin gwiwa, riƙon amana, girmama haƙƙin ɗan adam, da kuma gyaran tsarin gudanarwa da na kayan aiki domin inganta ayyukan Hukumar.

Shugaban ya bayyana cewa a ƙarƙashin jagorancin sa, DSS ta rarrabe tsakanin al’amuran al’umma da manyan laifuka kamar kisa ko tsaro, inda ya ce gogewarsa ta aiki ta nuna masa cewa a baya hukumar tana haɗa biyun ne waje ɗaya.

Ajayi ya bayana cewa, ba zai yiwu a yi amfani da ƙarfi a kan al’amuran jama’a, wanda hatta a cikin laifuka ba kowanne irin laifi ke buƙatar amfani da ƙarfi ba.

A lokacin da aka tambaye shi ko Hukumar a yanzu tana zuwa kotu ne a kan al’amuran jama’a, Ajayi ya ce, “Ƙwarai kuwa”.

“Na shaida wa abokan aiki na cewa kada a sake kama kowa a kan al’amuran da suka shafi jama’a, Kuma na tabbata kun ankara cewa, ko a shari’o’in da suka shafi yan jarida, mun gwammace mu tafi kotu saboda aiki guda muke yi”-

Ina kiranku abokan aikin mu, bambancin kawai shi ne, yayin da ku kuke sanar da jama’a, mu kuma muna sanar da Gwamnati bayanai ne a asirce, kafin daga bisani mu duba yiwuwar fitar da su ga jama’a.” Inji Shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *