Wadansu mutane da ake zargi da satar danyen mai su 37 sun mutu, sakamakon shaƙar wani mai mai guba da ke fitowa daga cikin jirgin dakon ɗanyen mai a yankin Okari Jetty, da ke Ƙaramar Hukumar Okrika a Jihar Ribas.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya faru da misalin kare 12 na daren ranar Alhamis, yayin da ake zargin ɓarayin man suna loda samfurin sa zuwa kwalekwalen su, daga wani babban jirgin dakon mai.
Jaridar ta ce lamarin ya faru ne sa’ad da wani katon jirgin dakon mai ya yada zango a wani bangare na gabar kogin, domin loda samfurin danyen man zuwa ƙetare, sai matasa fiye da 200 suka yiwa jirgin tsinke suna diba ta wani bangare dake zuba.
A cewar majiyar, yayin da ake tsaka da lodi akwai wari mai tsanani dake tashi, wanda ya kai ga fin karfin iskar dake kadawa a yankin.
Haka ce ta sanya matasa da dama yanke jiki suna faɗawa ruwa, yayin da wadanda suka tsira daga wurin ke samun kulawa a wani asibiti da ke birnin Fatakwal sakamakon matsalar sarkewar numfashi.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Darakta a wata Cibiyar kare haƙƙin matasa da muhalli (YEAC-Nigeria), Dr. Fyneface Dumnamene Fyneface, ya ce a ƙalla matasa 37 ne aka tabbatar da mutuwar su bayan shaƙar warin na man-samfurin “Indorama fuel”.
Daily Trust ta ruwaito cewa, da dama daga cikin wadanda ke da hannu a cikin lamarin ba a kai ga ganin su gansu ba bayan aukuwar lamarin da ya jijjiga daukacin karamar hukumar.