Babban Hafsan Sojojin Kasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya karbi wata babbar tawaga a Hedikwatar Rundunar Sojojin Kasa da ke Abuja, domin tattauna hanyoyin karfafa ayyukan kiwon lafiya da inganta kayayyakin more rayuwa na rundunar.
Tsohon Babban Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ne ya jagoranci tawagar da ta kai ziyarar, wadda ta kunshi wakilan kamfanoni masu zaman kansu da kuma masu ruwa da tsaki daga bangaren diflomasiyya na kasa da kasa.
- Masu satar danyen mai sun mutu a Ribas
- Babu ruwan DSS da abinda ke tsakanin farar hula-Ajayi
- Ana tuhumar wani mutum da laifin rusa allon tallan Tinubu
Taron ya mayar da hankali ne kan samar da wani tsayayyen Hadin Gwiwar Gwamnati da Kamfanoni Masu Zaman Kansu (PPP) domin bunkasa da zamanantar da cibiyoyin kiwon lafiyar Sojojin Najeriya.
Shirin hadin gwiwar ya kunshi yiwuwar ginawa da inganta asibitocin sojoji, samar da kayayyakin aikin likitanci na zamani, tallafawa samar da magunguna, da kuma amfani da fasahar zamani wajen gudanar da ayyukan kiwon lafiya a cibiyoyin rundunar.
A cewar bayanan, ana sa ran wannan hadin gwiwa zai kara karfin cibiyoyin kiwon lafiyar sojoji, da saukaka samun ingantaccen tsarin kula da lafiya ga jami’an sojoji da iyalansu.
Haka kuma, shirin na da manufar tabbatar da cewa asibitocin rundunar suna da karfin tunkarar kalubalen kiwon lafiya tare da samar da ingantaccen aiki mai dorewa.