An tsare wani mutun ɗan jihar Katsina, mai suna Aminu Sanda, wanda aka fi sani da Nesta, bisa laifin cin amanar ƙasa kan zargin rushe allunan tallan yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu.
Da farko dai ‘yan sanda a Katsina ne suka gayyaci Sanda, sannan suka tsare shi bisa zarginsa da cire allunan tallukan shugaban ƙasar da kuma kutse cikin ofishin jam’iyyar APC na jihar Katsina, tare zargin ya wawure kuɗi naira miliyan 35.
Sai dai Sanda ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa, ciki har da na cewa ya rushe allunan da kutsawa ofishin APC don sace kuɗin, zargin da Sanda ya bayyana a matsayin marasa tushe.
-
Majalisa ta wanke Gbajabiamila game da hannu a Hukumar bogi
-
Soji sun kwato makamai a Binuwai
-
NELFUND: Atiku ya yi alkawarin yafe bashi ga daliban Najeriya
Daga baya an miƙa Sanda zuwa shelkwatar ‘yan sanda ta ƙasa da ke Abuja, inda wata kotun majistare da ke Jiwa ta umurci da a cigaba da tsare shi bisa zargin cin amanar ƙasa.
Tun da farko, ‘Yan sanda ne suka bukatar neman cigaba da rike wanda ake zargin har tsawon makonni biyu domin su kammala bincike.
Amma a ranar Talata, lauyoyin Sanda sun halarci zaman kotun don neman belin sa, bukatar da masu shigar da kara suka yi akai da cewa suna son kotu ta bar musu shi na tsawon kwanaki 14 domin kammala bincike.
Ko da yake, Mai shari’a, Huzaifa Macchido, ya ce zai sanar da hukunci kan buƙatar masu kariya daga baya. wanda a cewar lauyoyin Sanda, jinkirin sanar da hukuncin ka iya bai wa ‘yan sanda damar cigaba da tsare shi.
A karshe kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Satumba domin duba buƙatar lauyoyin sa game da bayar da belin Sanda.