Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation WHIRL STROKE (OPWS) sun dakile wani yunƙurin ’yan bindiga tare da kashe ɗaya daga cikin su, tare da kwato makamai da alburusai a ƙaramar hukumar Katsina-Ala ta jihar Binuwai.

A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation WHIRL STROKE, Laftanar Ahmad Zubairu Zubairu, ya fitar ranar Laraba 2 ga Satumbar 2026, yace sunyi arangamar ne yayin wani sintiri da suka gudanar akan hanyar Gbise zuwa Igyudu.

Sanarwar ta bayyana cewa dakarun sun ci karo da wasu mutane biyu da ake zargi ’yan bindiga ne a kan babur, inda bayan tabbatar da cewa suna ɗauke da makamai, suka buɗe musu wuta inda daya ya tsere, daya kuma ya sheka lahira.

Rundunar ta ce bayan faruwar lamarin, dakarun sun gudanar da bincike da share fage a yankin domin tabbatar da tsaron al’ummomin da ke kusa.

Daga cikin kayayyakin da sojojin suka kwato sun haɗa da ƙaramar bindiga da harsashinta, kwanson harsashin AK-47 da nau’ikan alburusai daban-daban da wayar salula da wasu layu.

Rundunar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai kan motsin masu aikata laifuka.

Ta ƙara da cewa Operation WHIRL STROKE za ta ci gaba da gudanar da sintiri da ayyukan leƙen asiri domin wargaza ƙungiyoyin masu aikata laifuka da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan da take gudanar da ayyuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *