Hukumar Shige da Fice ta Gambiya ta tare mutane 46 da ake zargin na shirin yin hijira ba bisa ƙa’ida ba, a yankunan Brufut da Batokunku da ke yankin West Coast na ƙasar.

Sanarwar hukumar ta ce an gudanar da samamen ne a daren Litinin, 19 ga Oktoba, 2026, ta hannun jami’an sintiri na kan iyaka tare da haɗin gwiwar sashen kula da ƙaura da ke Tanji da taimakon abokan hulɗar shirin COP II.

Daga cikin mutanen da aka tare, 22 an same su a Batokunku, yayin da aka tare wasu 24 a Brufut.

Haka kuma, an kama wani da ake zargin mai safarar bakin haure ne, wanda ke taimaka wa jami’ai wajen gudanar da bincike.

Hukumar ta ce mutanen sun haɗa da ’yan Gambiya 23, ’yan Senegal 22 da ɗan ƙasar Guinea guda ɗaya. A cikinsu akwai maza 40, mata huɗu da ƙananan yara biyu.

Hukumar Shige da Fice ta Gambiya ta ce aikin na daga cikin ƙoƙarinta na kare rayuka da hana matasa shiga hijira ba bisa ƙa’ida ba, tare da ƙarfafa hanyoyin ƙaura masu aminci da bin doka.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *