Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi zargin cewa jami’an ’yan sandan Najeriya sun kashe wasu mutane ba bisa ƙa’ida ba, tare da kira da a tabbatar da hukunta masu laifi.
Ƙungiyar ta kawo misalin da Anthony Enruchi Obodo, mai shekaru 22, wanda ta ce jami’an ’yan sanda sun harbe har lahira a ranar 27 ga Agusta, 2026, yayin da yake tuƙa mota.
Amnesty International ta kuma ambaci kisan Mene Ogidi, mai shekaru 28, a Effurun ta Jihar Delta a ranar 26 ga Afrilu, 2026.
- Shekaru shida bayan zanga-zangar #EndSARS, Peter Obi ya sake neman a yi adalci ga waɗanda suka mutu a Lekki
- ’Yan sanda sun ceto mutane 18, shanu 20 a jihohi daban-daban
A cewar ƙungiyar, wani ɗan sanda ya harbe shi sau biyu bayan an danne shi a ƙasa.
Ƙungiyar ta ce a wasu irin waɗannan lamura da suka shafi zargin kashe mutane ba bisa ƙa’ida ba, azabtarwa da cin zarafi, hukumomi ba su ɗauki mataki ba duk da ƙoƙarin waɗanda abin ya shafa na neman adalci.
Amnesty International ta yi gargaɗin cewa rashin ɗaukar mataki kan irin waɗannan zarge-zarge na ƙarfafa rashin hukunta masu laifi, tare da buƙatar hukumomi su tabbatar da gudanar da bincike mai inganci da kuma hukunta duk wanda aka samu da laifi.