Rundunar ’yan sandan Najeriya ta ce jami’an tsaro sun ceto mutane 18 da aka yi garkuwa da su, tare da kwato shanu 20 da aka sace a wasu ayyukan tsaro da aka gudanar a jihohi daban-daban a ranar 20 ga Oktoba, 2026.
A jihar Benue, jami’an tsaro sun ceto mutane takwas daga hannun masu garkuwa da mutane a Onyangede, Ƙaramar Hukumar Otukpo, tare da kama waɗanda ake zargi biyu. A Kogi kuma, an ceto mutane 10 da aka sace a harin da aka kai wa wata mota a hanyar Kabba-Ayere.
A Sokoto, jami’an rundunar ’yan sandan tura-gaggawa da masu gadin al’umma sun fatattaki ’yan bindiga da suka kai hari ƙauyen Dukuma, Ƙaramar Hukumar Binji, inda suka kwato shanu 20 da maharan suka bari bayan sun tsere.
- Peter Obi ya ce ba ya adawa da tallafin ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ga iyalansu
- Shekaru shida bayan zanga-zangar #EndSARS, Peter Obi ya sake neman a yi adalci ga waɗanda suka mutu a Lekki
Sanarwar rundunar ta kuma ce an kashe wani da ake zargi da fashi da makami a Taraba bayan musayar wuta da sojoji, inda aka ƙwato bindiga da alburusai 15.
A Legas, an kama wani da ake zargi da fashi da makami a Satellite Town, tare da ƙwato bindiga da alburusai biyar.
A Akwa Ibom da Ebonyi, an kama mutum biyu da ake zargi da fashi da makami, tare da ƙwato makamai da wasu kayayyaki. Haka kuma, an kama wasu mutane 11 da ake zargi da aikata laifuka a Yaba da Orile a Legas, inda aka ƙwato abubuwan da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne.
A Osun da Enugu, ’yan sanda sun kama mutum uku da ake zargi da hannu a kisan gilla a Osun, da kuma mutum ɗaya kan wani kisan kai a Enugu.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike kan dukkan lamuran, yayin da ake neman sauran waɗanda suka tsere.