Dakarun Operation FANSAN YAMMA sun kuɓutar da mutane 27 da aka yi garkuwa da su tare da ƙwato babur guda ɗaya a wasu ayyukan tsaro da suka gudanar a Jihar Katsina.
Sanarwar da jami’in yaɗa labaran rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar a ranar 20 ga Oktoba, 2026, ta ce an sace mutanen ne a ranar 16 ga Oktoba a garin Gamji, Ƙaramar Hukumar Sabuwa.
Dakarun sashe rundunar na farko sun bi sawun maharan ta hanyar Gangare zuwa Kamba, inda suka yi arangama da su.
- Atiku ya zargi APC da kasa samar da adalci kan harin Lekki da sauƙin rayuwa ga matasa
- Tinubu ya ce ba zai dawo da tallafin man fetur ba
Rundunar ta ce ƙarfin wutar sojojin ya tilasta wa maharan guduwa tare da barin mutanen da suka sace.
Dukkan mutanen 27, waɗanda suka haɗa da maza 15 da mata 12, an kuɓutar da su ba tare da rauni ba. Bayan tantance su, an miƙa su ga shugabannin al’umma domin haɗa su da iyalansu.
A wani samame da aka gudanar a ranar a kusa da ƙauyen Kurba, Ƙaramar Hukumar Kankara, sojoji sun haɗu da wasu ’yan ta’adda a kan babura uku, amma sun tsere bayan ganin dakarun, inda suka bar babur guda ɗaya.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare domin dakile ayyukan ’yan ta’adda da dawo da zaman lafiya a Katsina da jihohin da ke maƙwabtaka da ita.