Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta dawo da tallafin man fetur ba, yana mai cewa matakin da ya ɗauka na cire tallafin ya zama dole domin gyara tattalin arzikin ƙasar.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ganawa da ƙungiyar City Boy Movement, wadda ke tallafa wa manufofin gwamnatinsa.
Ya ce da a ce an ci gaba da biyan tallafin, Najeriya za ta iya fuskantar matsalar rashin kuɗin gudanar da ayyukan gwamnati.
- Gambiya ta tare bakin haure 46 da ake zargin na shirin yin hijira ba bisa ƙa’ida ba
- Amnesty International ta bukaci a dauki mataki kan zargin kashe fararen hula da ’yan sanda ke yi
Shugaban ya yi amfani da misalin Annabi Musa (AS) da barin Masar, yana mai cewa ba za a nemi Annabi Musa ya koma Masar ba, domin nuna cewa gwamnatinsa ba za ta koma tsarin tallafin man fetur ba.
Ya kuma buƙaci mambobin ƙungiyar su yaɗa manufofi da nasarorin gwamnatinsa a jami’o’i, kasuwanni da ƙauyuka, tare da ƙarfafa matasa su mallaki katin zaɓe kuma su yi amfani da shi a zaɓe mai zuwa.
Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar da aka rantsar da shi a watan Mayun 2023.
Matakin ya jawo tashin farashin fetur da ƙarin tsadar rayuwa, inda farashin lita ɗaya ya kai tsakanin naira 1,350 da 1,405 a wasu manyan gidajen mai.