Kasar Norway, ta karbe iko da wani jirgin sojin ruwan Rasha a yankin Arctic, doa nufin tilasta wa kasar biyan diyya ga kamfanin makamashi na Ukraine, Naftogaz, sakamakon kwace kadarorin sa da Rashan ta yi a yankin Crimea.

Norway ta karbe iko da jirgin ne ranar Laraba, bayan da Moscow ta kasa biyan Naftogaz diyyar da ta kai dala biliyan 4.22, tare da kudaden ruwa, a matsayin diyya kan kadarorin kamfanin da Rasha ta kwace a Crimea.

A shekarar 2023 ne wata kotun dake shiga tsakani domin sasanta kasa da kasa ta yanke hukuncin cewa Rasha ta biya kamfanin Naftogaz diyyar kadarorin da ta kwace masa.

A cikin wani sako da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X, Naftogaz ya ce kwace jirgin na daga cikin kokarin da ake yi na tabbatar da hukuncin kotun sasantawar na kasa da kasa, da Naftogaz yayi nasara akai.

A cewar lauya David Pinsky da ke wakiltar Naftogaz, an kwace jirgin mai suna Professor Molchanov ne a yankin Svalbard na Arctic a kasar Norway,  bayan da wata cibiyar lauyoyin Amurka mai suna Covington ta shafe watanni tana bibiya da lura da duk inda jirgin yake kai komo.

Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Rasha, TASS, ya rawaito cewa wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Rasha na bayyana matakin da da aka dauka da “fashin teku.”

Jirgin Professor Molchanov na kasar Rasha ne da ake amfani da shi domin binciken ilmi da yawon buɗe ido. A shekarar 2014 ne Rasha, ta mamaye yankin Crimea tare hade shi da kasar ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *