Hukumomi a Jihar Neja, sun kama wasu ’yan kasar Chana huɗu, bisa zargin gudanar da aikin haƙar ma’adinai ba tare da izini ba a ƙauyen Mayaki da ke ƙaramar hukumar Lapai.
An kama mutanen ne bayan kwamishinan ma’aikatar albarkatun ma’adinai ta jihar, Muhammad Danjuma, ya kai ziyara yankin, bayan samun rahoto daga Sarkin Lapai Alhaji Umaru Bago Tafida, cewar wasu ’yan ƙasashen waje na haƙar ma’adinai a yankin.
Bayyanar rahoton ya sanya Sarkin ya umarci Hakimin gundumar kuma Chiroma Lapai Alhaji Mohammed Mustapha, ya bincika masa gaskiyar abiinda ke faruwa.
A ziyarar farko, an gano cewa gwamnatin jihar ba ta da masaniya kan al’amarin, wanda daga nan ne masarautar ta sanar da gwamnati halin da ake ciki, wanda nan take kwamishinan ma’adinai Honarabul Mohammed Qasim Danjuma ya ziyarci wajen.
Kwamishinan, ya buƙaci ’yan wadanda aka kama da su gabatar da lasisi da sauran takardun izinin gudanar da aikin, amma rahotanni sun tabbatar da cewa wadanda aka kama sun gaza samar da ingantattun takardun ko wata shaidar izini, sabo da haka gwamnatin Neja ta bayar da umarnin kama mutane huɗu daga ciki su.
Bayan mika su ga Rundunar tsaro fararen hula NSCDC, Kwamishinan ya kuma umarci al’ummar dake zaune a wurin su cigaba da sanya idanu kan kadarori da kayan aikin da ake haƙar ma’adinan da su, har sai an kammala bincike.
Ko a cikin watan Agustan shekarar 2026, kwamishinan ya gargadi mutane da kamfanoni da ke gudanar da irin wannan aiki da su dakatar da komai, ko kuma su fuskantar hukunci a gaban kotu, kwatankwacin yadda ta faru a farkon wannan shekara a wasu yankunan jihar.
Lamarin na Lapai, ya sake jawo hankali kan matsalar haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a Najeriya, duba da barazanar da hakan ke yi ga muhalli da asarar kuɗaɗen shiga ga gwamnati.
Gwamnatin Neja ta ja hankalin masu haƙar ma’adinai su mallaki lasisi, yayin da ma’aikatar albarkatun ma’adinai ta jihar ke cigaba da san idanu domin tabbatar da bin dokokin ƙasar.