Gwamnatin Jamus ta fito fili ta zargi Rasha da hannu a wani yunkurin harin ta’addanci da aka shirya, ta hanyar amfani da jirgi marar matuki makare da bama-bamai a kan wani babban filin jirgin sama a gabashin kasar.
Ministan Cikin Gida na Jamus, Alexander Dobrindt, ya ce Rasha ce ta kitsa yunkurin harin akan filin jirgin saman Leipzig/Halle a ranar 4 ga watan Agusta, wanda a sakamakon haka Berlin ta dauki matakin rufe ofishin jakadancin Rashan dake Bonn kafin 18 ga watan Satumba.


Kasashe da dama a nahiyar Turai da ke bai wa Ukraine goyon baya suna fuskantar karuwar laifukan da suka shafi zagon kasa tun bayan fara yakin Ukraine.

[Hoto:Kyiv Post]
Yayin da Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da Kungiyar Tsaro ta NATO suka yi alkawarin ba da cikakken goyon baya, an gano cewa filin jirgin saman na Leipzig shi ne babbar cibiyar sarrafa kayan agaji da makamai zuwa Ukraine.
